Thursday 27 November 2025 - 10:50
Shugaban Jami'atul Al-Mustafa ya halarci taron Ƙungiyar Tsofaffin ɗaliban Jami'ar Almustafa reshen Indonesia

Hauza/An gudanar da taron Kungiyar Tsofaffin ɗaliban Jami'ar Al-Mustafa na Indonesia, zaman wanda Shugaban Jami'ar Al-Mustafa ya halarta ya gudana ne a Hussainiyyar Ƙurba, yankin Suyuv Pandan. 

A cikin rahoton ɓangaren fassara na ofishin labarai na Hawzah, Hujjatul-Islam wal-Muslimin Al-Abbasi ya jaddada muhimmancin ƙirƙirar sabbin abubuwa, haɗin kai, da haɓaka ƙwarewar tsofaffin ɗaliban na Jami'ar Al-Mustafa, domin su sami damar fuskantar ƙalubalen zamani.

Ya kuma nuna godiya ga ƙoƙarin da  da malamai da masu aikin hidima ga addini suka yi wajen hidima ga al'umma da ƙasa. Ya kuma yaba da gudunmawar da Hujjatul-Islam Nasser Demiati da Zahr Yahya suka bayar ta hanyar tsara ayyuka cikin ilmi.

Shugaban Jami'ar Al-Mustafa ya bayyana cewa: "Babu shakka, aikinmu shi ne tallafawa tsofaffin ɗaliban da cibiyoyin da suka kafa. Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (Dz) mai girma yana ci gaba da aikin  bin sawun Imam Khomeini (RA) na kafa cibiyoyin ilmi musamman ga ɗaliban ƙasashen waje. Mu wani ɓangare ne kawai na wannan babban aiki, kuma alhamdulillah, mun iya yin hidima ga dubun-dubatar ɗalibai daga ƙasashe sama da 120."

Shugaban ya kuma jaddada cewa tsarin ilimin na Hawzah na da shi kaɗai bai isa ya biya buƙatun wannan zamani ba. Ya ce: "Ba mu cewa komai ya cika ba, amma muna shirye da mu ci gaba da bin  tafarkin gyara da ci gaba."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha